ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Labarai

Nijeriya Za Ta Gudanar da Taron Farko na IPI Afrika – Minista

Nijeriya ta amince da karɓar baƙuncin babban taron farko na ƙasashen nahiyar Afrika na Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Duniya (IPI).

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a wurin wani taro da aka gudanar a birnin Vienna na ƙasar Austriya, inda ya gana da Shugaban Kwamitin Zartarwa na IPI, Mista Marton Gergely; da Daraktan Zartarwa na IPI, Mista Scott Griffen, da kuma wakilin Nijeriya da Afrika a hukumar, wato Mista Raheem Adedoyin.

A cewar sa, “Nijeriya ta amince da gudanar da taron farko na ƙungiyar ta sashen nahiyar Afrika. Wani babban abin girmamawa ne a gare mu mu yi jagoranci kamar yadda muka saba.”

Wannan sanarwar ta biyo bayan matakin hukumar IPI na kafa ƙungiyoyin yankuna domin kula da buƙatu na musamman na kowane yanki a cikin al’ummar IPI ta duniya.

Ministan ya kuma tunatar da membobin yadda Nijeriya ta gudanar da babban taron duniya na IPI a Abuja a shekarar 2018 cikin nasara, inda ya ce ƙasar nan ta shirya sosai don sake gudanar da wani taron.

Ko da yake ba a saka ranar taron ba tukuna, Mista Griffen ya bayyana cewa ofishin IPI da ke Vienna zai tsara cikakkun bayanai tare da Mista Adedoyin da kuma Kwamitin IPI na Nijeriya.

Shugaban Kwamitin Zartarwar IPI, Mista Gergely, ya yaba wa Nijeriya a matsayin jagora wajen tafiyar da dimokiraɗiyya da kuma kare ’yancin ’yan jarida.

Haka zalika, Mista Griffen ya jinjina wa Kwamitin IPI na Nijeriya bisa jajircewar su wajen kare ’yancin manema labarai.

A yayin tattaunawar, Ministan ya jawo hankalin shugabannin na IPI kan buƙatar ƙarin tallafin ƙungiyar ga Makarantar Koyon Aikin Jarida ta Nijeriya (NIJ) da ke Ogba, Legas — makarantar da IPI ta kafa tun a cikin 1971 a lokacin jagorancin marigayi Alhaji Lateef Jakande.

Ya bayyana cewa yanzu haka tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Aremo Olusegun Osoba, shi ne shugaban kwamitin gudanarwar makarantar.

Idris, wanda yana ɗaya daga cikin manyan membobin IPI, ya kasance cikin mahalarta babban taron IPI na duniya da bikin cikar ƙungiyar shekara 75 da aka gudanar a Vienna.

Sauran ’yan tawagar Nijeriya a taron sun haɗa da Mista Raheem Adedoyin; da Shugaban IPI Nijeriya, Musikilu Mojeed; da tsohon mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu; da Dakta Fabian Benjamin na JAMB; da Babban Sakatare ga Gwamnan Jihar Kwara, Malam Rafiu Ajakaye; da Shugaban kamfani da jaridar Patrons Media/The Culture, Mista Steve Ayorinde; da Farfesa Abigail Ogwuensi na Jami’ar Legas; da lauya kuma mai bada shawara ga IPI Nijeriya, Mista Tobi Soniyi.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *