Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu yau da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a birnin London, bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Shugaba Tinubu ya kuma miƙa ta’aziyya ga matar marigayin, Hajiya Aisha Buhari tare da mika sakon alhini da juyayi a madadin kansa da gwamnatin Najeriya.
A wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayar da umarni ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da ya tashi zuwa Birtaniya domin jagorantar dawo da gawar marigayin zuwa gida Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance shugaban ƙasa sau biyu karkashin mulkin dimokuraɗiyya bayan nasarar zaɓen 2015 da na 2019, kuma ya rike matsayin Shugaban Mulkin Soja daga watan Janairu 1984 zuwa watan Agusta 1985.
Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarni da a kafa tutocin Najeriya a tsakiya domin girmamawa da mutunta rayuwar wannan babban jagora da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar ƙasa.