Sojojin rundunar hadin gwiwa ta Operation MESA a Jihar Kano sun yi nasarar dakile wani yunkurin hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Shanono, a yammacin ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamba, 2025.
A cewar sanarwar da rundunar ta 3 Brigade ta fitar, sojojin tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kan motsin ‘yan bindiga da suka shigo yankunan Unguwan Tudu, Unguwan Tsamiya da Goron Dutse da misalin karfe biyar na yamma.
Sanarwar ta ce, “Sojojinmu sun yi artabu da ‘yan bindigar da suka shigo kan babura, kuma bayan musayar wuta mai tsanani, an fatattake su daga yankin. Sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga 19, tare da kwato wasu babura da wayoyi guda biyu.”
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa sojoji biyu da wani ɗan sa-kai (Vigilante) sun rasa rayukansu yayin musayar wutar.
Sojojin sun ce har yanzu suna ci gaba da aikin sintiri da tunkarar sauran ‘yan bindigar da ke barazana ga al’ummar yankin, musamman masu fama da matsalar satar shanu.
Kwamandan Brigade ta 3, Brigediya Janar Ahmed Tukur, ya tabbatar wa jama’a da cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Ya kuma roƙi al’umma da su kasance masu faɗakarwa da yin gaggawar sanar da hukumomi idan suka ga wani motsi ko mutumin da suke zargi.
