ASHAFA MURNAI BARKIYA
Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai ba da fifiko ga ƙarfafa sa ido kan bankuna, daƙile hauhawar farashi, sabunta tsarin biyan kuɗi, da gyaran tsare-tsare na cikin gida a shekarar 2026, kamar yadda Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya tabbatar.
Cardoso ya ce Babban Bankin Nijeriya zai ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa kulawa da sa ido kan harkokin bankuna da inganta ƙa’idojin shugabanci, tare da gyara tsarin sa ido kan hauhawar farashi, domin cimma daidaitaccen farashi mai dorewa.
Ya ce CBN na shirin sabunta tsarin biyan kuɗi na Nijeriya domin inganta inganci da faɗaɗa tsarin shigar ɗimbin jama’a cikin harkokin kuɗi.
Haka kuma, bankin zai tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙiren fasahar kuɗi (fintech) bisa ƙa’idoji da ke kare masu amfani da kuma tabbatar da ingancin tsarin kuɗi.
“Yayin da muke shiga shekarar 2026, manufofin mu a bayyane suke: za mu ci gaba da ƙarfafa tsarin banki ta hanyar tsauraran matakan sa ido da kyakkyawan shugabanci,” inji Cardoso a wani rubutu da ya wallafa a shafin X a ranar Asabar.
“Za mu inganta tsarin sa ido kan hauhawar farashi domin samar da daidaitaccen farashi mai ɗorewa; mu sabunta tsarin biyan kuɗi domin ƙara inganci da haɗa jama’a; sannan mu ƙarfafa kirkire-kirkiren fintech cikin tsari mai kula da kare masu amfani da kuma amincin tsarin kuɗi.”
Cardoso ya ƙara da cewa bankin zai ci gaba da gina ƙwarewa da ƙarfin aiki a cikin CBN, ta hanyar amfani da bayanai da kayan aikin fasahar ƙirƙirekirikire na zamani, wato AI domin samun saurin aiwatarwa, amsawa cikin gaggawa da kuma ingantaccen aiki.
Ya ce bankin zai zurfafa haɗin gwiwar dabaru da za su ƙarfafa sahihanci da martabar Nijeriya a matsayin bankin ƙasa mai hangen nesa da amincewa.
Gwamnan CBN ya kuma jaddada cewa gyare-gyare za su ci gaba da mayar da hankali kan kwanciyar hankali da bunƙasar tattalin arziki na dogon zango, yana mai cewa aiwatarwa cikin tsari da daidaito na da matuƙar muhimmanci wajen samun sakamako mai ɗorewa.
“Gyara tsari hanya ce da ke buƙatar daidaito da jajircewa. Yayin da sabuwar shekara ke farawa, hankalin mu yana nan daram: kare amincewa, tabbatar da kwanciyar hankali, da kafa tubalan bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa a Nijeriya. Ina yi muku fatan alheri da nasara a sabuwar shekara.”
