Shirin Shugaba Tinubu na rangwamen kuɗin wanke ƙoda ya amfanar marasa lafiya da dama a Jihar Kano

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin rage kuɗin wanke koda daga ₦50,000 zuwa ₦12,000, ragin da ya kai sama da kashi 76 cikin ɗari. Wannan mataki na daga cikin manufofin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Tinubu domin sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa samun kiwon lafiya mai ingancin da sauƙi.

Rahotanni daga Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) sun nuna cewa yawan marasa lafiya da ke zuwa neman jinya ya ƙaru sosai tun bayan da aka rage kuɗin. A cewar Tijjani Rahim, Mataimakin Daraktan Sashen Ma’aikatan Jinya (Nas) da ke kula da sashen wanke koda, yanzu ana duba marasa lafiya 22 zuwa 25 a kowace rana.

Wani mara lafiya, Sani Musa, ya ce kafin rangwamen yana biyan kuɗi tsakanin ₦54,000 da ₦60,000 a kowane zama. Ya ce daga baya aka rage shi zuwa ₦20,000 kafin yanzu ya sauka zuwa ₦12,000. Shi ma Mamuda Aliyu ya bayyana cewa ragin ya ba shi damar ci gaba da jinya. Haka zalika, Hafiza Isa ta ce a baya tana biyan ₦60,000, daga baya ₦55,000, sannan ₦45,000, kafin a rage zuwa ₦20,000.

A nasa jawabin, Shugaban Asibitin AKTH, Abdurrahman Sheshe, ya tabbatar da fara shirin rangwamen a Kano, inda aka tura kayan aiki da za su iya ɗaukar zama 1,000 na wanke koda.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin ƙaddamar da shirin National Emergency Medical Services and Ambulance Scheme (NEMSAS) a asibitin, wanda zai bai wa mata masu juna biyu, yara, waɗanda suka samu haɗari da sauran ayyukan gaggawa damar samun awanni 48 na jinya kyauta da sufuri na gaggawa.

Shirin rangwamen wanke koda na cikin tsare-tsaren gyaran kiwon lafiya da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa, ciki har da Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) da kuma NEMSAS.

A ranar 21 ga Agusta 2025, gwamnatin tarayya ta amince da shirin a manyan asibitoci 11 na tarayya da ke fadin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *