ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Labarai

Shugaba Tinubu ya gana da Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kan halin da ake ciki na tsaro a sassan ƙasar

Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi takaitaccen jawabi daga Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Tosin Adeola Ajayi, a daren Juma’a kan halin da ake ciki na tsaro a sassan ƙasar.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Ajayi ya gabatar wa Shugaban Ƙasa cikakken bayani game da sabbin bayanan sirri da hukumar ta tattara kan matsalolin tsaro, ciki har da hare-haren ’yan bindiga a wasu jihohi da kuma matakan da jami’an tsaro ke ɗauka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya dage tafiyarsa zuwa taron kolin G20 da EU–AU da za a gudanar a Kudancin Afirka da Angola, domin dai ya ci gaba da samun cikakken bayani da kuma jagorantar matakan gaggawa da ake ɗauka kan batutuwan tsaro, musamman lamarin sace dalibai a wasu yankuna.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu ya jaddada cewa babu wani aiki da ya fi muhimmanci ga gwamnatinsa kamar kare rayuwar ’yan ƙasa, kuma saboda haka ya zauna a ƙasar domin ya tabbatar an karfafa aikin hadin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro.

Shugaban ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da dukkan ƙarfinta wajen ganin an kawo ƙarshen hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa jama’a, tare da tabbatar da cewa daliban da aka sace a jihohin Arewa maso Yamma sun komo gida lafiya.

Hukumomin tsaro na ƙasar sun ce za su cigaba da aiki kafada da kafada domin tabbatar da tsaron rayuka, yayin da ake kara shigar da sabbin jami’ai da kayan aiki a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *