Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ganawar ta gudana ne kafin babban taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa NEC na jam’iyyar da za a gudanar a ranar Alhamis a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban ƙasa.
Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, wanda ke jagorantar Ƙungiyar Gwamnonin APC (Progressive Governors Forum), ne ya jagoranci sauran gwamnonin zuwa wannan taro da aka gudanar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana cewa ganawar na da nufin karfafa jam’iyya da kuma inganta kyakkyawan shugabanci a matakin jihohi da ƙasa baki ɗaya. Ya ce sun tattauna hanyoyin da za a bi wajen ƙarfafa jam’iyyar daga tushe, tun daga matakin ƙananan hukumomi, zuwa jihohi har zuwa ƙasa baki ɗaya.
A kan yiwuwar fitowar sabbin matakai ko sauye-sauye daga taron na NEC, Uzodimma ya ce: “Ba za mu iya hango abin da za a cimma ba har sai mun isa wurin taron gobe.” An dai tsara taron NEC domin duba manyan batutuwan da suka shafi jam’iyyar da kuma tsara sabbin dabarun ƙarfafa haɗin kai da shugabanci mai tasiri.
Daga cikin muhimman abubuwan da ake sa ran taron zai warware har da batun nada sabon shugaban jam’iyya na ƙasa, biyo bayan murabus din Dr. Abdullahi Umar Ganduje a watan Yuni.