Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Namadi Sambo, murna bisa nadin sa da aka yi a matsayin Sardaunan Zazzau daga Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.
Nadin ya gudana ne a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, a Zariya, Jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya bayyana wannan mukami da cewa yana da matuƙar daraja a al’adu da tarihi na Arewacin Najeriya, kuma ya nuna yadda masarautar Zazzau ta amince da basira, gaskiya da jajircewar Namadi Sambo wajen ci gaban al’umma.
Shugaban ya ce wannan girmamawa alama ce ta jagoranci nagari da gudummawar Sambo ga cigaban ƙasa tun daga lokacin da ya rike manyan mukamai a gwamnati.
Ya kuma yabawa Sarkin Zazzau bisa ci gaba da riƙe al’adar girmama mutanen da suka yi fice wajen jagoranci, kishin ƙasa da kuma ɗorewar zaman lafiya.
Shugaba Tinubu ya yi fatan Allah ya ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa nasara a sabuwar rawar da zai taka, tare da kira gare shi da ya ci gaba da zama abin koyi ga matasa da kuma yin aiki kafada da kafada da shugabannin gargajiya domin ci gaban al’umma da ƙasar baki ɗaya.