Sojojin Yemen sun kai hari kan jirgin ruwan yakin Amurka na USS Harry S. Truman

Sojojin Yemen sun bayyana cewa sun kaddamar da wani sabon hari kan Amurka, harin a kan jirgin ruwan yakin Amurka ne da ke kwasar jiragen sama na yaki da ke tekun “Red Sea” a karo na uku a cikin awanni 24.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta Press TV ta ruwaito, a cikin wani jawabi da rundunar sojojin ta Yemen ta fitar a ranar Talata ta bayyana cewa sakamakon harin Amurka kan Yemen, “Sojojin ruwa, sojojin da ke kula da makaman roka da sojojin saman mu sun kai hari kan jiragen ruwan da suke a matsayin barazana, ciki har da jirgin ruwan yakin Amurka mai kwasar jiragen sama na USS Harry S. Truman, ta hanyar amfani da makamai masu linzami da dama da kuma jiragen yaki marasa matuka.”

“Wannan na cigaba a yanzu haka da muke wannan jawabin, wanda hakan ke nuni da kashi na uku na wannan aikin a cikin awanni 24.” Kamar yadda jawabin ya kara da cewa.

“Hare-haren mu kan makiyiya Amurka za su cigaba, a kan jiragen ruwan yakin su a yankin da aka ayyana cikin tsanantawa, da yardar Allah.” Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

Sojojin sun ma bayyana cewa hare-haren Yemen a kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila (HKI) za su cigaba ta hanyar hana jiragen ruwan na HKI wucewa a tekun “Red Sea” da sauran tekun Arabiya tare da kai hare-hare a kan sojoji da wuraren ta masu muhimmanci.

“Bayan haka, hare-haren sojinmu kan makiyiya HKI, ta hanyar hana tafiye-tafiyen ta a tekun “Red Sea” da tekun Arabiya tare da kai hari kan soji da wuraren ta masu muhimmanci, wanda hakan na da niyyar dakatar da kisan kare dangin ta ne a kan raunana mutanen Falasdinawa na Gaza – wani laifi da aka yi a kan idon Larabawa, musulmai da duka duniya.” Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

Sun jaddada cewa hare-hare kan HKI din za su cigaba har sai gwamnatin HKI din ta dakatar da kisan kare dangin ta kan raunana Falasdinawa kuma ta dakatar da zagayewar da ta yiwa yankin.

A cikin daren ranar Lahadi, sojojin Yemen suka bayyana bugo jirgi mara matukin Amurka na US MQ-9 kan yankin mulki na Ma’rib, wannan kuwa shine jirgi mara matuki na 16 da kasar ta bugo tun bayan 7 ga watan Oktobar 2023.

A cikin daren ranar Lahadi, Amurka ta kai hare-hare da dama a kan kasar Yemen da niyyar tursasa kasar ta Larabawa ta dakatar da goyon bayan ta ga Falasdinawan Gaza.

Jiragen yakin Amurka sun kaddamar da manyan hare-hare goma sha uku a kan babban birnin Yemen, Sana’a.

Kafofin watsa labarun Yemen sun ruwaito hare-hare takwas a yankin Al-Malikah da ke Sana’a da kuma hare-hare biyar a yankin Sarf.

Hare-haren na zuwa ne bayan hare-haren da suka yi sanadiyyar rasuwar farin hula mutum daya tare da jikkata mutane goma sha biyu a gundumomi biyu na Sana’a.

Mafi yawan hare-haren na Amurka an yi su ne a kan gine-ginen fararen hula da ke babban birnin kasar ta Yemen.

Hare-haren Yemen din dai sun haifar da kulle tashar jiragen ruwan Eilat da ke kudancin HKI din inda hakan ya haifar da babban koma baya ga tattalin arzukin ‘yan HKI din.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *