‘Za mu Ci Gaba da Yaƙar Masu Kashe Masallata da Kirista a Najeriya’

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da walwala da samar da kayan yaƙi ga rundunar sojin Najeriya don ci gaba da yaƙar ta’addanci

Da yake jawabi a wajen bikin zagayowar ranar sojoji karo na 162 a Kaduna, Tinubu wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya tabbatar wa sojojin da cikakken goyon bayansa wajen tunkarar ‘yan ta’adda da kuma fatattakar su.

Shugaban ya misalta ƴan ta’addan da marasa imani, da basu martaba addini ko ƙabila, inda ya ce gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaƙarsu

Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da saka hannun jari a fannin samar da kayan aikin soji na zamani, da kafofin bayanan sirri, da samar da walawala ga rundunar don tabbatar da cewa jami’anta basu rasa makamai da kwarewa ba.

Shugaban ya amince da kalubalen tsaro da ke barazana ga zaman lafiya da hadin kan al’ummar kasar, waɗanda suka haɗa da ta’addanci, tayar da ƙayar baya, da ‘yan fashin daji da masu tayar da zaune tsaye.

Shugaban ya bukaci sojojin Najeriya da su ƙara zage damtse tare da ba su tabbacin cikakken goyon bayansa da na ‘yan Najeriya.

Shugaban ya jinjina wa jaruman da suka riga mu gidan gaskiya tare da jajanta wa iyalansu, inda ya basu tabbacin ci gaba da tunawa da su na har abada.

“Kuna da cikakken izinina da na al’ummar Najeriya kan fatattakar masu zagon kasa a ƙasarmu,” in ji Tinubu.

“Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya, kada mu miƙa makomarta ga rarrabuwar kawuna, ko nuna halin ko-in-kula”

Taron ya samu halartar manyan baki da dama da suka hada da tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon, gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, da Ministocin Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, sai shugaban hafsan soji Laftanar Janar Olufemi Oluyede.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *