Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da rabon kayan noman tallafi ga manoma a jihohi daban-daban na arewa domin ƙarfafa samar da abinci da rage dogaro da shigo da kayayyakin gona daga ƙasashen waje.
A yan kwanakin da suka gabata, gwamnatin ta raba kayan aikin gona da irin shinkafa, masara da taki ga manoma a jihohin Adamawa, Bauchi, Nasarawa da Taraba.
A jihar Adamawa, akalla ƙungiyoyin manoma 30 ne suka amfana da shirin, inda aka basu taki da injinan ban-ruwa don ƙarfafa noman rani.
Haka zalika a jihar Bauchi, an raba kayan noma ga manoma ƙanana da gwamnati ta ce za su taimaka wajen ƙara samar da abinci da bunƙasa tattalin arziki.
A jihar Nasarawa, ƙungiyoyi 25 na manoma ne suka karɓi kayan aiki da iri don shuka, yayin da a Taraba aka fara rabawa ga ƙungiyoyi 200 na manoma domin ƙarfafa noman haɗin gwiwa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Tarayya ta ce tana da niyyar mayar da hankali kan samar da abinci da tallafawa manoma a duk faɗin ƙasar nan.
Masana harkar noma na ganin irin waɗannan shirye-shiryen tallafi za su taimaka matuƙa wajen rage hauhawar farashin kayan abinci da kuma bunƙasa noman cikin gida.