ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2024

Gwamna Abba ya yi fusata da yadda aikin raba abincin azumi ke gudana a birnin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, ya nuna ɓacin ran sa ganin yadda ake tafiyar da aikin dafawa, rabawa da kuma rashin ingancin abincin azumi ke gudana a cikin birnin Kano. Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna,…

DARE ƊAYA ALLAH KAN YI BATURE’: Gwamna Namadi ya bai wa mutum 27 ramcen Naira miliyan 270, domin kama sana’ar zama miloniya

A ƙoƙarin sa na ganin ya cika alƙawarin da ya ɗauka tun farkon hawa mulkin sa cewa, zai buɗa wa mutum 150 hanyoyin kama sana’ar zama miliyoya a zangon sa na farko, Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya bai…

Sojojin Isra’ila sun takaita isa masallacin Al-Aksa ga masu ibada

Rundunar sojin Isra’ila ta hana daruruwan masu gudanar da ibada kaiwa ga masallacin Al-Aksa da ke Jerusalem da aka mamaye domin yin sallar Juma’a ta biyu a cikin wata mai tsarki na Ramadana, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na WAFA…

IPOB ta yi gargadi ga gwamnatin Tinubu, kar Kanu ya mutu a tsare

Kungiyar da ke fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB) ta yi ikirarin cewa gwamnatin Nijeriya na son kashe shugaban ta, Nnamdi Kanu, a sashen tsare mutane na jami’an tsaron farin kaya (DSS), inda ta yi gargadin akwai abinda zai biyo baya…

Ku yi amanna da Tinubu, matsaloli za su ƙare, inji Ministan Yaɗa Labarai

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri su yi imani da gwamnatin Tinubu. Idris ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin buɗa baki da ya yi…

Gwamna Dauda Lawal ya ce ilimi ne ginshikin ci gaban Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ayyana ilimi a matsayin wani ginshiƙi mafi muhimmanci ga ci gaban jihar Zamfara. A Larabar nan ne ɗaliban makarantar ‘Leadsprings International Schools’ suka karrama Gwamna Lawal a gidan gwamnati da ke Gusau. Kamar yadda…

Falasdinawa 31,819 aka kashe, 73,934 suka jikkata a Gaza – Ma’aikatar lafiya

Akalla Falasdinawa 31,819 aka kashe kuma 73,934 suka jikkata tun 7 ga watan Oktoba sakamakon yakin Isra’ila a zirin Gaza, kamar yadda ma’aikatar lafiya a zirin ta bayyana a ranar Talata. Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, Falasdinawa 93…

Gwamnan Zamfara zai inganta Asibitin Kwararru na Yariman Bakura

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da shirin gyara, tare da sake inganta asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da ke Gusau domin magance ƙalubalen da ake fuskanta na samar da ingantacciyar kiwon lafiya a Jihar Zamfara. Gwamnan ya amince…

Masu garkuwa da Daliban Kaduna sun nemi a ba su naira biliyan 1 kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da yaran makaranta a jihar Kaduna sun yi magana da kakakin iyalan wadanda suka kama, inda suka nemi a basu naira biliyan 1 (dalar Amurka 620,432) domin su sako yaran. Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Reuters…

Gwamnatin Zamfara ta faranta wa ma’aikata saboda Ramadan

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da biyan ma’aikatan Jihar kuɗaɗen su na hutu a matsayin wata garaɓasa ta musamman albarkacin watan Ramadan. A ranar Laraba ne ma’aikatan gwamnatin Jihar da na Ƙananan Hukumomi a Zamfara suka fara karɓar…