ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2024

Tinubu ya dawo gida bayan ya kai ziyara Ƙatar

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauka Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai a ƙasar Ƙatar. Jirgin shugaban ƙasa, mai lamba NAF 001, ya sauka a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 7 na…

Gwamnatin Jihar Zamfara ta tantance ma’aikata 3,079 da suka yi ritaya don biyan su fensho

Gwamnatin Jihar Zamfara ta tantance ma’aikata 3,079 da suka yi ritaya a ƙoƙarinta na biyan basukan da gwamnatocin baya suka bari. Ma’aikatan jihar da na Ƙananan Hukumomi da suka yi ritaya a Zamfara ba su samu haƙƙoƙin su ba tun…

Gwamnan Zamfara ya samu yabo daga Ministan Ayyuka

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samu yabo daga Ministan Ayyuka, David Umahi, bisa gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a ayyukan sabunta birane. A ranar Juma’ar da ta gabata ne Ministan ya kai ziyarar aiki Jihar Zamfara a…

An duba lafiyar sama da mutum 2,213 kyauta a Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala kashi na uku na Shirin Inganta Lafiyar al’umma Kyauta, inda aka duba mutane sama da 2,213. Shirin na musamman da aka fara a watan Yulin bara, an samu nasarar duba lafiyar mutane masu fama da…

Gwamnan Zamfara ya ce bunkasa ilimi na cikin ajandodinsa shida

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ƙara jaddada cewa ilimi na ɗaya daga cikin ajandodi shida da ya sanya a gaba, ganin cewa ilimi ginshiƙin dukkan wayewa ne. A lokacin gudanar da wani biki ranar Larabar nan a Gusau, Gwamna…

Gwamnati ba za ta yi amfani da rahoton kwamitin Oronsaye don ta kori ma’aikata ba – Idris

Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta yanke shawarar yin amfani da rahoton yi wa ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya garambawul na kwamitin Steve Oronsaye domin a rage yawan kashe kuɗaɗe wajen tafiyar da ayyukan gwamnati ne. Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar…

Yan Houthi sun shirya domin haramta duk wani jirgin ruwa da ya shafi Isra’ila, wanda yake mallakin Amurka, Ingila

Kungiyar ‘yan Houthi da ke Yemen sun sanar da haramtawa jiragen ruwan da suka shafi Isra’ila da kuma wadanda suke mallakin Amurka da Ingila wucewa ta tekun Red Sea. Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, duk wani jirgin ruwan…

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce yawan wadanda suka rasu a yakin ya kai 29,410

Ma’aikatar lafiya da ke Gaza a ranar Alhamis ta bayyana cewa akalla mutane 29,410 aka kashe a yankin Falasdinawa yayin yaki a zirin. Kamar yadda kafar watsa labaru ta The New Arab ta ruwaito, wani jawabin ma’aikatar ya ce mutane…

Jagoran harkar musulunci a Nijeriya ya dawo gida Nijeriya

Jagoran harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya dawo gida Nijeriya daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar yadda yake a cikin wani sako da ofishin Shehin Malamin ya wallafa a kafar sada zumunta ta Facebook,Shaikh Zakzaky ya dawo ne a ranar…

Sojan saman Amurka ya mutu bayan ya sa wa kan sa wuta a kofar ofishin jakadanci Isra’ila

Wani sojan saman Amurka ya mutu bayan ya sawa kan sa wuta a ranar Lahadi a kofar ofishin jakadancin Isra’ila da ke Washington, D.C. Kamar yadda kafar watsa labaru ta The New Arab ta ruwaito, wani bidiyo da aka wallafa…