ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2024

Bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai: Sauye-sauyen Tinubu na da nufin mayar da Nijeriya mai ƙarfin tattalin arziƙi – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Shugaban Ƙasa Tinubu na aiwatar da wasu tsare-tsare da sauye-sauye da aka tsara domin magance kura-kuran da aka yi a baya da kuma sanya Nijeriya ta zama…

Yarjejeniyar Samoa: Gwamnatin Tarayya ta yaba da hukuncin NMCC kan rahoton bogi da jaridar Trust ta buga

Gwamnatin Tarayya ta yaba wa Hukumar Yaƙi Da Ƙorafe-ƙorafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (National Media Complaints Commission, NMCC), mai kula da harkokin yaɗa labarai a Nijeriya, kan hukuncin da ta yanke a kan jaridar Daily Trust dangane da rahoton bogi…

MATSALAR TSARO: Kiran APC Na A Sanya Dokar Ta-baci A Zamfara Shirme Ne, Da Raina Al’ummar Jihar Zamfara – PDP A Zamfara

Jami’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ta bayyana kiran da jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan jihar Bello Matawalle da Sanata Abdulaziz Yari suka yi na kafa dokar ta-baci a Zamfara a matsayin “hassada” da ci gaban da aka samu a…

AMBALIYAR RUWA: GWAMNAN ZAMFARA YA JAJANTA WA GWAMNATIN BORNO, YA BA DA GUDUNMAWAR MILIYAN N100 GA WAƊANDA ABIN YA SHAFA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri. A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Mallam Abubakar Nakwada, Sakataren Gwamnatin Jihar…

Nijeriya za ta haɗa gwiwa da Amurka wajen inganta ‘yancin ‘yan jarida da yaƙi da baza labaran bogi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana ƙudirin ma’aikatar sa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin ƙasar Amurka domin inganta ‘yancin manema labarai a Nijeriya. Rabi’u Ibrahim, mai taimaka wa ministan kan harkokin…

Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa rundunar sojojin ƙasar nan jajircewar gwamnatinsa wajen bai wa jami’an soji cikakken goyon baya

Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa rundunar sojojin ƙasar nan jajircewar gwamnatinsa wajen bai wa jami’an soji cikakken goyon bayan gwamnatin sa a jihar Zamfara. Ranar Juma’ar nan da ta gabata ne Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin Babban Hafsan tsaron…

Gwamnan Zamfara ya nuna matuƙar jimamin sa game da ibtila’in haɗarin jirgin ruwa

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna matuƙar jimamin sa game da ibtila’in haɗarin jirgin ruwan da ya faru a Ƙaramar Hukumar Gummi ta jihar. Da sanyin safiyar ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgin ruwa mai ɗauke da…

GWAMNA LAWAL YA BA DA CIKAKKEN GURBIN KARATU GA ƊALIBAI MASU HAZAƘA NA ZAMFARA, YA SHA ALWASHIN BUNƘASA ILIMI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayar da tallafin karatu ga haziƙan ɗalibai 30 na Zamfara a makarantar Gwamnatin Tarayya da ke Suleja. Gwamna Lawal ya yi wannan alwashin ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da ya karɓi…

GWAMNA LAWAL YA BA DA SAMA DA NAIRA BILIYAN 11 DON AIKIN INGANTA ILIMIN ’YA’YA MATA A ZAMFARA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da shirin raba maƙudan kuɗaɗe ga Ƙanana da Matsakaitan Makarantu (SIGS) a ƙarƙashin shirin Samar da Ilimi da Ƙarfafa ’Ya’ya Mata (AGILE) a jihar. A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan ya…

Gwamnatin Tarayya ta kusa ƙaddamar da shirin Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa, inji Minista

Gwamnatin Tarayya ta fara himmar ƙaddamar da shirin nan na Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa, da nufin bunƙasa ɗabi’u, ɗa’a da kuma farfaɗo da al’adu a Nijeriya. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana…