ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai

Ministocin gwamnatin Tinubu za su fara gabatar da ayyukan da suka yi ko suka sa a gaba a Tarukan Manema Labarai na Ministoci na shekarar 2025 a ranar Juma’a, mai zuwa, 21 ga Fabrairu. Ma’aikatar Yaɗa da Wayar da Kai…

Gwamnatin Tarayya ta yi alhinin rasuwar dattijo Edwin Clark

Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan rasuwar dattijo ɗan kishin ƙasa kuma tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Tarayya, wato Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru 97. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata,…

Murar tsuntsaye ta bulla a jihar Filato, ta kashe tsuntsaye 300

“Avian influenza” a turance wadda aka fi sani da murar tsuntsaye, ta kashe tsuntsaye 300 a wata gona da ke jihar Filato. Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, babban jami’in kula da dabbobi na jihar, Dakta Shase’et Sipak, ne ya bayyana…

Shirin Amurka na tayar da mutanen Gaza ba zai je ko’ina ba – Khamenei

Ayatollah Ali Khamenei a ranar Talata ya yi watsi da shawarar Amurka na tayar da Falasdinawa daga zirin Gaza wanda yaki ya yiwa illa, inda ya ce “ba zai je ko’ina ba.” Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, Sayyid…

Kasar Sin za ta bayar da taimakon jin kai ga iyalai 60,000 da ke Gaza

Hukumar cigaban kasa-da-kasa ta kasar Sin ta bayyana cewa za ta bayar da taimakon jin kai ga iyalai 60,000 da ke Gaza, kamar yadda wani rahoto na The New Arab ya nuna. “A duk yadda al’amari ya juya, Sin za…

Yawan mutanen da suka rasu ya karu zuwa 14 a ambaliyar ruwan Amurka

Akalla mutane 14, ciki har da yaro, suka rasu yayin da ake fuskantar ambaliyar ruwa mai tsanani sakamakon ruwan sama mai karfi a wasu bangarorin kasar Amurka. Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, an tabbatar da rasuwar mutane 12 a…

Cututtuka na kara yaduwa a Gaza sakamakon karancin ruwa – Oxfam

Kungiyar Oxfam ta yi gargadi kan kara yaduwar da cututtuka sakamakon tsananin rashin tsaftataccen ruwa ke yi a Gaza da kuma sokawe da ba a yi gyara kansa ba da ya cika ya ke gudu a kan titunan zirin, kamar…

Gwamnatin Tarayya na neman sauƙaƙa tsarin ba da biza don ƙarfafa kasuwancin ‘yan Nijeriya a duniya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ƙasashen duniya da su sauƙaƙa tsarin ba da biza ga kamfanonin Nijeriya da ke ƙoƙarin kafa masana’antu da kasuwanci a ƙetare. Ministan ya yi wannan kira ne a…

NAFDAC ta rufe shaguna 3000 a Legas, ta kama motoci 12 na magungunan bogi

Hukumar da ke sa ido a kan abinci da magungunan ta Nijeriya (NAFDAC) ta kulle shaguna 3000 a Idumota Open Market da ke Legas a makon farko na gudanar da ayyukan ta. Kamar yadda Channels ta ruwaito, kamar yadda wani…

SAƘO DAGA MOHAMMED IDRIS, MINISTAN YAƊA LABARAI DA WAYAR DA KAI

A wannan rana ta Lahadi, na wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ganawa da shugabannin ƙungiyar jama’ar Nijeriya mazauna ƙasar Habasha. Wannan dama ce da muka samu muka ji matsalolin su tare kuma da ba su tabbacin cewa gwamnati za…