Akalla mutane 14, ciki har da yaro, suka rasu yayin da ake fuskantar ambaliyar ruwa mai tsanani sakamakon ruwan sama mai karfi a wasu bangarorin kasar Amurka.
Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, an tabbatar da rasuwar mutane 12 a jihar yamma-maso-gabas ta Kentucky, yayin da wasu biyu kuma aka tabbatar da rasuwar su a jihohin Georgia da West Virginia.
“Na samu wasu labarai masu tsauri.” Kamar yadda gwamnan Kentucky, Andy Beshear, ya bayyana a shafin X a ranar Litinin.
“Yawan wadanda suka rasu yanzu a Kentucky ya karu zuwa 12. Dole mu tuna, wannan ba kawai alkaluma bane wannan mutanen Kentucky ne wadanda iyalansu da masoyansu za su rasa.”
Yawan wadanda suka rasu a jihar ya karu zuwa takwas, ciki har da yaro dan shekara 7, ranar Lahadi.
Mutum daya ma ya rasu a jihar Georgia, kamar yadda jaridar Atlanta Journal-Constitution, ta ruwaito a ranar Lahadi inda ta bayyana samo bayanin daga kafofin cikin gida.
Gwamnan jihar West Virginia, Patrick Morrisey, shima ya tabbatar da jikkatar mutum daya a jihar sa yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Litinin. Wasu da dama sun bace yayin da ake tsaka da da fuskantar “ambaliyar ruwa wadda ta kai wani mataki” kamar yadda ya kara da cewa.
Ruwan mai karfi wanda ya fara a ranar Asabar ya shafi jihohi da dama da suka hada da Kentucky, Tennessee, Georgia, Arkansas, Virginia da West Virginia.