Gwamnatin tarayya ta biya wa ɗaliban jami’ar Dutsin-Ma fiye da dubu 10 kuɗin makaranta

A ci gaba da aiwatar da shirin lamunin karatu na Tallafin Kuɗin Karatu ta Ƙasa (NELFUND) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, jihar Katsina, ta tabbatar da karɓar Naira biliyan ɗaya da miliyan sittin da biyar da dubu ɗari uku da casa’in da ɗaya (₦1,065,391,000) domin biyan kuɗin makaranta na dalibanta.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da jami’ar ta fitar, wadda ke ɗauke da sa hannun Muƙaddashin Shugaban Makarantar, Farfesa Aminu Ado. A cewar takardar, kuɗaɗen za su biya kuɗin karatun dalibai 10,018 da suka cancanci samun tallafin a wannan zangon karatu.

Wannan mataki ya zo daidai lokacin da ɗalibai da iyayensu ke fuskantar matsin tattalin arziki, kuma zai taimaka wajen saukaka nauyin kuɗin makaranta, da kuma karfafa damar koyo da cigaba a fannin ilimi.

Shirin NELFUND dai na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na tallafa wa fannin ilimi, ta hanyar samar da lamunin karatu da za a biya a hankali bayan kammala karatu da samun aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *