Hukumar Kwastan ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa ta karɓi umarnin Ma’aikatar Kudi na dakatar da aiwatar da harajin kashi 4% na Farashin kaya kafin ɗauko su daga ƙasar da aka samo su wato Free-on-Board (FOB) da aka ɗora kan kayayyakin da ake shigo da su ƙasar nan.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Abdullahi Maiwada, ya fitar a ranar Litinin, hukumar ta ce tana godiya da wannan matakin da Ma’aikatar Kudi ta ɗauka tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da bin manufofin gwamnati na tattalin arziƙi.
Dr Maiwada ya ce hukumar ta fara tattaunawa da Ma’aikatar Kudi domin tabbatar da cewa ba a samu cikas a ayyukan hukumar ba.
Hukumar ta kuma yi karin haske kan rahotannin da ke yaɗuwa a kafafen yaɗa labarai cewa harajin kashi 4% na FOB ƙirƙiro shi a kayi a ‘yan kwanakin nan. Ta ce wannan tanadi ne na doka da Majalisar Tarayya ta kafa a cikin Sashe na 18(1)(a) na Dokar Hukumar Kwastan ta 2023, wanda ya tanadi cewa “ba za a karɓi kasa da kashi 4% na FOB ba akan kayayyakin da ake shigo da su, bisa tsarin da duniya ke bi.”
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, tare da tabbatar da sauƙaƙe cinikayya da kuma ƙara samun kudaden shiga ga gwamnati.
“Muna da kwarin gwiwa cewa tattaunawa da Ma’aikatar Kudi da sauran masu ruwa da tsaki za su samar da mafita da za ta fi amfani ga Najeriya baki ɗaya, ta hanyar ƙara samun kudaden shiga da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa,” in ji sanarwar.
Hukumar Kwastan ta ce za ta ci gaba da aiki da ‘yan kasuwa, masu fitar da kaya da hukumomin ƙasa da ƙasa wajen tabbatar da gudanar da ayyuka cikin bin ƙa’idoji.
