Rubutawa: Aliyu Samba
Akwai wata tsohuwar ka’ida a ilimin siyasa da ake kira “Diversionary Theory of War”, wadda ke bayyana cewa wasu gwamnatoci na iya shiga cikin rikicin wasu ƙasashe ko ƙirƙirar barazana daga waje don karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin cikin gida. Wannan dabarar tana taimakawa wajen haɗa kan al’umma da dasa musu kishin ƙasa, musamman idan gwamnati na fuskantar rikice-rikice ko rarrabuwar kawuna a cikin gida.
Wannan ne ainihin abin da ake gani Shugaban Amurka Donald Trump ke aikatawa a halin yanzu, amfani da Najeriya a matsayin abar lakacewa hanci don ya samu hanyar ceto kansa daga matsalolin cikin gida da kuma tabbatar da tasirinsa a idon magoya baya.
Dalilai Masu Tabbatar da hakan sun haɗa da:
- Rikicin Cikin Gida da Majalisar Wakilai (House of Representatives). Trump yana cikin matsananciyar takaddama da Majalisar Wakilai ta Amurka, duk kuwa da cewa jam’iyyarsa ta Republican ke da rinjaye. Sabani kan kasafin kuɗi, ikon mulki, da tsoma baki cikin harkokin majalisa sun haifar da rabuwar kawuna a cikin jam’iyyar. Wannan ya rage masa iko, ya kuma bar shi cikin yanayi da ke buƙatar ya samo sabuwar hanya don dawo da martaba da haɗin kai a cikin jam’iyyarsa.
Ta fuskar dabarar “Diversionary Strategy”, irin wannan yanayi yakan sa shugabanni su kirkiri barazana daga waje don jawo hankalin jama’a su manta da rikicin cikin gida. A wannan karon, Trump ya zabi Najeriya a matsayin abin zargi ta hanyar kirkirar labarin cewa ana kisan kare dangi ga mabiya addinin Kirista a kasar, wani ikirari da ba shi da tushe ko hujjar da za ta iya tabbatar da shi.
Dalilan Siyasa da Dabarun “Geopolitical Strategy” na Amurka
A tarihi, Amurka ta yi amfani da wannan salon wajen tabbatar da tasirinta a duniya:
- A Iraki (2003), ta kirkiri hujjar makaman kare dangi don fara yaƙi, daga baya aka tabbatar da cewa hujjar ƙarya ce.
- A lokacin Yaƙin (Cold War), ta shiga cikin harkokin Vietnam, Chile, da Nicaragua don kare muradunta.
- Bayan harin 9/11, ta fara yaƙi da “ta’addanci” a Afghanistan da Iraki domin haɗa kan jama’ar ta.
Yanzu kuma, Trump na ƙoƙarin amfani da wannan salo wajen farfado da tasirin Amurka a Afirka, ta hanyar yin amfani da Najeriya a matsayin misali na “ƙasar da ake zargin take zaluntar Kiristoci.” Wannan ya dace da yadda yake amfani da manufarsa ta “America First”, wato kare Amurka da darajarta ta hanyar rage ƙimar wasu ƙasashe.
Dalilan da ke Tabbatar da Cewa Wannan Dabara na Nufin Kassara Najeriya Kai Tsaye;
- Shigar Najeriya cikin BRICS:
Matakin Najeriya na shiga haɗin gwiwar tattalin arziki na BRICS (Brazil, Russia, India, China, South Africa) ya nuna ƙoƙarinta na rabuwa daga dogaro da tsarin tattalin arzikin yammacin duniya da Amurka ke jagoranta. Wannan babban juyi ne wanda ya tayar da hankalin Trump da masu ra’ayinsa na adawa da China da Rasha. - Goyon bayan Falasdinu: Najeriya ta bayyana matsayinta na gocewa goyon bayan kai tsaye ga Isra’ila tare da jaddada cewa tana marawa Falasdinu baya kan manufar ƙasa biyu. Wannan ya saba wa ra’ayoyin Trump wanda ya daɗe yana amfani da goyon bayan Isra’ila don samun farin jini a cikin Amurkawa.
- Sake tsari a tattalin arziki: Tinubu ya ɗauki sabbin matakai na sake fasalin tattalin arzikin ƙasa ta hanyar sassauta canjin kuɗi, jawo jarin ƙasashen gabas, da rage dogaro da tallafin Amurka. Wannan ya zama abin da ke ɗora Najeriya a sahun ƙasashen da ke neman ‘yancin tattalin arziki, wanda ke da barazana ga tasirin Amurka a yankin.
- Trump da dabarar ƙarya a kafafen labarai: A cikin siyasar sa, Trump ya shahara da amfani da ƙarya da bayanan yaudara (disinformation) don jawo hankalin jama’a. Zargin sa na cewa ana “kashe Kiristoci a Najeriya” ya dace da irin wannan salo, manufarsa ita ce bata sunan Najeriya, ƙirƙirar labarin tausayi, da jawo magoya baya na addinin kiristanci a Amurka.
Mu dawo mu kalli gaskiyar Abin Da Ke Faruwa.
Najeriya tana fuskantar matsalolin tsaro da ta’addanci da ke da dalilai da dama, wani lokacin bisa dalilin siyasa, wanj lokacin bisa dalilin tattalin arziki, ko kabilanci, ba iya rikicin addini kawai ba. Masu aikata laifukan ba wai suna wakiltar wani addini bane, kuma gwamnati na kokarin shawo kan matsalar a matakai daban-daban.
Don haka, zargin Trump na cewa ana yin “genocide” ga Kiristoci a Najeriya, ba wai kawai ƙarya ba ce, illa ma yana da nufin rage darajar Najeriya a idon duniya, tayar da hankali, da rage amincewar kasashen duniya da shugabancin Tinubu.
Me Ya Kamata Najeriya Ta Yi
- Ƙarfafa huldar diflomasiyya da kasashen gabas da na BRICS, don tabbatar da cikakken ‘yanci a fannin tattalin arziki.
- Amfani da kafafen yada labarai na duniya wajen fayyace gaskiyar lamarin tsaron Najeriya da wanzar da bayanai na gaskiya.
- Shirya takardun hujjoji da bayanai na ƙasa da ƙasa don kare martabar kasar a Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran cibiyoyin kasa da kasa.
- Gina hadin kai a cikin gida domin kada ra’ayoyin addini ko siyasa su zama makamin da wasu ke amfani da shi don kawo rarrabuwar kawuna.
A halin yanzu, Trump yana amfani da tsohuwar dabarar “Diversionary Theory of War”, wato kirkirar barazana daga waje domin kau da hankali daga matsalolinsa na cikin gida. Zargin da yake yi wa Najeriya game da “kisan kiyashi ga mabiya addinin kiristanci” wani ƙoƙari ne na siyasa da yaudara domin ya tabbatar da tasirin Amurka da kuma ceto kansa daga matsin lamba a cikin gida.
Najeriya dole ta fahimci cewa wannan dabarar ba wai kawai magana ce ta siyasa ba, amma ƙoƙari ne na lalata martabarta da tasirinta a duniya. Don haka, tsare muradun ƙasa da ƙimar Najeriya ne babbar mafita.
~Aliyu Samba
4th Nov, 2025
