Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da bai wa sabuwar Jami’ar Kimiyyar Likitanci da Fasahar Lafiya ta Tarayya da ke Tsafe cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar kafuwarta da ci gabanta.
A ranar Litinin ne Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibrahim Yakasai, tare da tawagar shugabannin jami’ar suka kai ziyarar ban-girma ga gwamnan a gidan gwamnati da ke Gusau.
Yayin da yake maraba da tawagar, Gwamna Lawal ya tunatar da cewa gwamnatin sa ta ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi da lafiya domin farfaɗo da waɗannan muhimman fannoni biyu.
Ya ce, “Ina maraba da ku a gidan gwamnati. Wannan shi ne karo na farko da muke ganawa a hukumance kan wannan jami’a da aka kafa kwanan nan. Kamar yadda kuka sani, gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a fannonin ilimi da lafiya — kuma wannan jami’a ta haɗa bangarorin biyu. Duk da cewa makaranta ce, tana mai da hankali ne kan harkokin kiwon lafiya. Lafiya muhimmin fanni ne wanda gwamnati ke son ta inganta.”
Gwamnan ya bayyana cewa an ware filin da ya kai kusan kadada huɗu don ayyukan raya jami’ar, kuma gwamnatin sa ta riga ta zuba fiye da naira biliyan takwas a cikin aikin gina makarantar.
Ya ƙara da cewa, “A matsayina na shugaba mai alhakin jama’a, zan tabbatar jami’ar ta samu duk abin da take bukata don ta fara aiki cikin nasara. Za mu ci gaba da neman ƙarin tallafi, kuma dukanmu muna tare da ku domin tabbatar da wannan burin.”
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibrahim Yakasai, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa jajircewarsa wajen farfaɗo da harkokin ilimi da lafiya a jihar.
Ya ce, “Na yi zagaye a wasu asibitocin jihar Zamfara, kuma na ga irin ayyukan da ka kammala — tabbas kana da ƙwarewa da jajircewar da ake buƙata don tabbatar da nasarar wannan jami’a. Wannan ita ce jami’a ta farko a Nijeriya da ta mayar da hankali gaba ɗaya kan kimiyyar lafiya da fasahar likitanci.”
Farfesa Yakasai ya bayyana cewa matsalar da ake fama da ita a Nijeriya ita ce ƙarancin kayan aikin likitanci na zamani, amma jami’ar Tsafe za ta taimaka wajen cike wannan gibi. Ya ƙara da cewa jami’ar ta shirya fara aiki, kuma yana da cikakken tabbacin goyon bayan gwamnati.
Sulaiman Bala Idris
Mai Magana Da Yawun Gwamnan Zamfara
10 ga Nuwamba, 2025
