ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Labarai

Tawagar da Gwamnatin Tarayya ta tura zuwa Amurka tana samun nasarar magance labaran ƙarya game da yanayin tsaron Nijeriya, inji Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tawagar manyan jami’an Gwamnatin Tarayya da ta tafi ƙasar Amurka a ƙarƙashin jagorancin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, tana gudanar da aiki sosai wajen magance labaran da ake yaɗawa na ƙarya da ke nuna wai ana cin zarafin addinai a Nijeriya.

“Ba mu bar sarari ga yaɗa bayanan karya ba. Jami’an mu suna Washington da hujjoji, bayanai, da saƙo a fili cewa babu wani cin zarafi ko danniya da gwamnati ke yi wa kowace ƙungiyar addini a Nijeriya,” inji Idris a wata hira da aka yi da shi a Politics Today na gidan talbijin na Channels, wadda aka watsa a yammacin Asabar.

Ministan ya bayyana cewa tawagar manyan jami’an Nijeriya da ke Amurka sun gana da Sakataren Yaƙi na Amurka, membobin Majalisar Dokokin Amurka, jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, da sauran muhimman shugabannin ƙasar, inda suka gabatar da hujjojin gaskiya game da ƙalubalen tsaron Nijeriya, tare da yin cikakken bayani kan yaƙi da ta’addanci, haɗin gwiwar hukumomin tsaro, da ƙoƙarin kare ’yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

A cewar Ministan, waɗannan tattaunawar suna da matuƙar muhimmanci wajen gyara ra’ayoyin da aka yi wa ƙarin gishiri a cikin tattaunawar majalisa da yaƙin neman goyon bayan ƙungiyoyi na baya-bayan nan.

Ya ce: “Manufar mu a bayyane take… Muna nuna wa abokan hulɗar mu cikakken bayani game da halin tsaro, matakan da gwamnati ke ɗauka, da kuma cewa ’yan ta’adda sun kashe Kiristoci da Musulmi. Labaran da ake yaɗawa na kisan ƙare dangi ba daidai ba ne, kuma suna da haɗari.”

Ministan ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana ɗaukar wannan lamari da matuƙar muhimmanci, inda ba kawai ya ƙarfafa tsarin tsaro na cikin gida ba, har ma ya faɗaɗa haɗin kai da ƙasashen duniya domin tallafa wa yaƙi da ta’addanci da harkokin leƙen asiri.

Ya ce aikace-aikacen da tawagar ke yi na nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na kare martabar Nijeriya da tabbatar da cewa abokan hulɗa na ƙasashen waje suna yanke shawara bisa bayanan da aka tantance, ba kan labaran gefe guda ba.

Ya jaddada cewa dangantakar Nijeriya da Amurka tana ƙarfi, kuma waɗannan mu’amalar suna nuna buɗaɗɗen salon gwamnatin Tinubu na tattaunawa, haɗin kai, da fayyace gaskiya.

Ya kuma bayyana cewa ana sa ran gudanar da ƙarin tarurruka a kwanaki masu zuwa a matsayin wani ɓangare na tsare-tsaren gwamnati na kare gaskiya a game da haƙiƙanin halin tsaron Nijeriya.

Idris ya buƙaci ’yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su, tare da tabbatar wa da jama’a cewa gwamnati za ta ci gaba da yaƙi da rashin tsaro, tare da ci gaba da hulɗa da ƙasashen duniya don tabbatar da cewa a fagen duniya ana gabatar da sahihin labari a kan Nijeriya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *