China ta bayyana goyon baya ga Najeriya tare da gargaɗin tsoma bakin ƙasashen waje kan zargin tauye ‘yancin addini

Gwamnatin China ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Najeriya a yayin da ake samun zazzafar muhawara bayan suka daga Amurka kan yadda gwamnatin Najeriya ke tafiyar da batutuwan addini a cikin ƙasa.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta China, Mao Ning, ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin ma’aikatar ranar Talata, inda ta ce kasarta na adawa da duk wani ƙoƙarin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kowace ƙasa, musamman da sunan kare ‘yancin addini ko ɗan Adam.

“A matsayinta na abokiyar hulɗa ta dabarun ci gaba da Najeriya, China na cikakken goyon bayan gwamnatin Najeriya wajen jagorantar al’ummarta bisa tsarin da ya dace da halin da ƙasar take ciki,” in ji Mao Ning.

“Muna adawa da duk wata ƙasa da ke tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashe da sunan addini ko kare ‘yancin ɗan Adam. Muna kuma adawa da barazanar sanya takunkumi ko amfani da ƙarfi don tilastawa wata ƙasa bin wata hanya.”

Wannan matsayi na China na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Najeriya a matsayin “ƙasa mai matsala ta musamman” saboda, a cewarsa, ana zaluntar mabiya addinin Kirista a ƙasar.

Trump ya yi barazanar cewa Amurka na iya dakatar da duk wani taimako ga Najeriya, ko ma ta ɗauki matakin soja idan gwamnatin Najeriya “ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci.”

Masana harkokin diflomasiyya sun bayyana cewa kalaman Trump na iya dagula dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya, musamman ganin yadda China ke ƙara karfafa hulɗar tattalin arziki da diflomasiyya da Najeriya a ƙarƙashin tsarin BRICS.

China ta kasance ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar tattalin arziki na Najeriya, tana zuba jari a fannoni da dama kamar makamashi, gine-gine da fasahar, tare da nuna goyon bayan siyasa da diflomasiyya ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *