Gwamnatin Tarayya Ta Tura Ƙarin Jami’an Tsaro Don Murƙushe Ta’addanci – Ministan Yaɗa Labarai
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kudurinta na ƙara tsananta yaki da ta’addanci da aikata laifuka a sassa daban-daban na ƙasar, bayan jerin hare-haren da suka faru kwanan nan.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Radio House, Abuja, ranar Laraba 19 ga Nuwamba, 2025, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar dan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗaga matakin sha’anin tsaro zuwa matsayi mafi girma domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
Ministan ya miƙa sakon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa, yana mai bayyana kashe babban hafsan soji, sace dalibai a Jihar Kebbi da harin da aka kai cocin Eruku a Kwara a matsayin “abu mai muni” game da barazanar da ƙasar ke fuskanta.
Ya ce Shugaba Tinubu ya dage tafiyarsa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu da wasu tarukan ƙasashen waje, domin mai da hankali kan batutuwan tsaron cikin gida. Haka kuma ya umarci rundunonin soji da ‘yan sanda su tura ƙarin jami’ai zuwa Eruku da yankin ƙaramar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.
Ministan ya ƙara da cewa: “Jami’an tsaronmu sun samu umarni na musamman wajen ceto daliban makarantar Kebbi da gaggawa, tare da tarwatsa duk wata hanyar sadarwa ta ‘yan ta’adda a faɗin ƙasa.”
A cewar Idris, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, na can Birnin Kebbi bisa umarnin Shugaban Ƙasa, yana ganawa da Gwamnan Jihar Kebbi, shugabannin tsaro, sarakunan gargajiya, da iyalan daliban da aka sace.
Ministan ya kuma yi watsi da ƙoƙarin da wasu ke yi na bai wa rikicin fassarar addini, yana mai cewa matsalolin tsaro a Najeriya sun shafi musulmi da kirista, da kabilu daban-daban.
“A wannan lokaci, haɗin kan ƙasa shi ne kayan aikinmu mafi ƙarfi,” in ji shi. “Dole ne mu guji ƙiyayya da rarrabuwar kawuna. Abokan gaba na gaskiya su ne ‘yan ta’adda da miyagun da ke ƙoƙarin tayar da hankalin ƙasa.”
Ya jaddada matsayin Najeriya a matsayin ƙasa mai addinai daban-daban, inda ‘yancin bauta ke cikin kundin tsarin mulki. Ya kuma kira jama’a da su tallafa wa jami’an tsaro, yana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin ganin an kubutar da ɗaliban da aka sace tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.





