Gwamnatin Tinubu ta mayar da martani kan matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ’yancin addini

Gwamnatin Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake ganin suna take ’yancin yin addini.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris (FNIPR), ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Cibiyar Ƙasa ta Yaɗa Labarai, Abuja, a ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025.

Idris ya ce gwamnatin Najeriya ta san irin damuwar da wannan mataki na Amurka ya haifar, musamman ma bayan furucin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar kai farmaki kan Najeriya bisa hujjar kariya ga Kiristoci.

Ministan ya jaddada cewa matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta ba su taɓa bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba, inda ya ce:

“Ta’addanci ba ya da addini, ba ya kallon ƙabila ko matsayi. Yaƙi ne da dukkan mutanen da ke son zaman lafiya a Najeriya.”

Ya ƙara da cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakai na zahiri don kawo ƙarshen matsalar tsaro, kuma tun bayan hawansa mulki a watan Mayu 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna tsantsar niyyarsa ta tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.

A cewar Ministan, sojojin Najeriya sun kashe sama da ’yan ta’adda 13,500, tare da kama fiye da 17,000 da ake ci gaba da bincike da shari’a a kansu, haka kuma an ceto mutum 9,800 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara.

Idris ya bayyana cewa sauyin da aka yi wa manyan hafsoshin tsaro da kuma sake tsara tsarin tsaro a ƙasar na daga cikin matakan Shugaba Tinubu na kawo kwarin gwiwa da inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.

“Manufar ita ce a tabbatar da cewa kowace kusurwa ta Najeriya ta samu tsaro, kuma kowanne ɗan ƙasa ya rayu cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa an samu raguwar hare-haren ta’addanci sosai musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, tare da raunin kashi 80 cikin 100 na hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a Kudu maso Gabas.

Gwamnati ta ce an kama wasu manyan shugabannin ƙungiyoyin ta’addanci kamar Mahmud Muhammad Usman da Abubakar Abba na ƙungiyar Ansaru, da kuma Khalid Al-Barnawi, wanda ake zargi da kitsa harin ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Abuja a 2011.

Ya ƙara da cewa mutum 125 daga cikin waɗanda ake zargi da ta’addanci sun riga sun sami hukunci, yayin da wasu daruruwan ke ci gaba da fuskantar shari’a a kotuna daban-daban.

Duk da matakin Amurka, Ministan ya ce Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da Amurka da sauran ƙasashe domin kawar da ta’addanci, yana mai cewa:

“Muna fatan Amurka za ta fahimci cewa Najeriya ƙasa ce mai girma, mai ɗimbin al’adu da addinai, wacce ke samun ci gaba a fannin tsaro da tattalin arziki.”

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya samar da jiragen yaki na Super Tucano da ake amfani da su wajen yaƙi da ’yan ta’adda, kuma nan gaba kadan Ana sa ran ƙarin jirage masu sarrafa makamai za su iso ƙasar.

A ƙarshe, Idris ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tana mai cewa:

“Najeriya tana hannun aminci da shugabanci mai cike da kwarin gwiwa. Shugaba Tinubu na jagorantar tsaro, ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya mai dorewa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *