ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Labarai

Hukumar da ke kula da ayyukan Hukumar Tsaron Ƙasa ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci rubuta jarabawar na’ura mai ƙwaƙwalwa (CBT)

Hukumar da ke kula da ayyukan Hukumar Tsaron Ƙasa, Hukumar Gidan Gyaran Hali, Hukumar Kashe Gobara, da Hukumar Shige da Fice (CDCFIB) ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci rubuta jarabawar na’ura mai ƙwaƙwalwa (CBT) domin daukar sabbin ma’aikata a hukumomin tsaron da ke ƙarƙashinta.

A cikin wata sanarwa da sakataren hukumar, Manjo Janar Abdulmalik Jubril (mai ritaya) ya fitar a Abuja ranar Laraba, ya bayyana cewa, hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Hukumar Kula da gidan gyaran hali ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa, Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa da kuma Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Civil Defence.

Sanarwar ta ce duk masu neman gurbin aiki a ɗaya daga cikin waɗannan hukumomi su ziyarci shafin hukumar na yanar gizo wato https://recruitment.cdcfib.gov.ng daga ranar Alhamis, 30 ga Oktoba, domin tantance ko sun samu gurbin zuwa mataki na gaba.

Hukumar ta kuma gargadi masu nema da su tabbatar da amfani da shafin da aka bayar kawai domin gujewa fadawa hannun ’yan damfara.

Daukar sabbin ma’aikatan dai yana daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa hukumomin tsaro da kuma samar da damar aikin yi ga matasa a fadin ƙasar.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *