Kasar Sin ta gargadi Amurka da Indiya da su gujewa amfani da kasar Sin wajen yin fito-na-fito ta hadaka biyo bayan sanarwar Amurka na kara yawan sayar da makamai ga Indiya.
Kamar yadda Press TV ta ruwaito, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen wajen Sin, Guo Jiakun ya yi gargadi ga Washington da ta kauracewa amfani da “fito-na-fito” da Sin domin samun daidaitawa a yayin sayar da kaya.
“A wajen samar da dangantaka da kuma hadin kai a tsakanin kasashe, abu ne mai muhimmanci kada a yi amfani da Sin a matsayin wadda ake tattaunawa a kan ta, kuma bai kamata ya zama dama ta ruruta siyasar kungiyanci ba da kuma hadaka domin yin fito-na-fito.” Kamar yadda Guo ya bayyana a wani bangaren jawabin da ya gabatar.
Firaministan Indiya, Nerandra Modi, dai ya tafi Washington ne a wannan makon domin yin ziyara ta kwana biyu da niyyar hana yakin safara (Trade War) da Trump.
Sai dai, Trump ya yi amfani da wannan damar ta ziyara domin sayar da makaman soji da Amurka ta kera ga Modi.
Amurka da Indiya suna bangaren wata hadaka ne da ta hada da Japan da Australia a karkashin shirin Washington na tunkarar Sin, kamar yadda Press TV ta ruwaito.
Masana sun yi imanin cewa yunkurin Trump na yarjejeniyar sayar da makamai ga Indiya da aka kiyasata ta kai ta biliyoyin dalalo na yin nuni da wani babban mataki ne dangane da hadakar soji a tsakanin Washington da New Delhi.
Sanarwar ta Trump na zuwa ne bayan ganawarsa da Modi a Washington inda suka tattauna abubuwa da dama ciki harda safara, shigowar jama’a cikin kasa da tsaro na kasa-da-kasa.
“Farawa daga wannan shekarar, za mu yi kari dangane da makaman da muke sayarwa Indiya na biliyoyin daloli,” kamar yadda Trump ya bayyana yayin wata tattaunawa da ‘yan jaridu ta hadaka da Modi, “Za ma mu samar da hanyar samarwa Indiya jiragen saman yaki na F-35 stealth.”
Daga baya, sakataren harkokin kasashen wajen Indiya, Vikram Misri, ya fayyace cewa yarjejeniyar jirgin yakin F-35 na a matakin shiri ne, ba a fara ba a hukumance.
Kasar Indiya ta kasance babbar mai sayen kayan yaki daga Amurka, inda tuni ta sayi makaman da Amurka ta kera na sama da dalar Amurka biliyan 20 tun shekarar 2008.
Kasar Sin ta nuna damuwa dangane da fadada kawancen soji tsakanin Amurka da kawayenta da ke yankin Indiya da tekun “Pacific.”
Manyan jami’an kasar Sin sun ce hadakar soji tsakanin Amurka da kasashen yankin Asiya da “Pacific” zai iya kawo matsala ga zaman lafiya da daidaito a yankin, wanda zai haifar da fada na kasa-da-kasa.