Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 a Borno da Yobe

Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 tare da dakile hare-hare da dama da aka kai kan sansanonin sojoji a jihohin Borno da Yobe.

Rundunar sojin ta ce ‘yan ta’addan sun kai hare-hare a lokaci guda tsakanin daren Alhamis da wayewar gari, inda suka afka wa sansanonin sojoji a Dikwa, Mafa, Gajibo da Katarko, waɗanda ke ƙarƙashin sashe na 1 da 2 na rundunar hadin gwiwa ta farko.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar hadin gwiwar Arewa maso Gabas, Lt.-Col. Sani Uba, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri a ranar Alhamis.

Ya ce sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan bayan wani dogon artabu, tare da hare-hare ta sama da kuma jajircewar dakarun ƙasa.

“Sojojinmu sun kashe ‘yan ta’adda sama da 50, kuma sun kwato manyan makamai da dama,” in ji Lt.-Col. Uba.

A cewarsa, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda 38, bindigogin PKT guda bakwai, makaman RPG guda biyar, da gurneti da kuma tarin albarusai.

Majiyoyi daga cikin jami’an tsaro sun kuma shaida wa jaridar Premium Times cewa sojojin sun yi artabu da mayakan ISWAP a garuruwan Mafa da Dikwa na jihar Borno, inda aka samu asara a bangarorin biyu.

Rundunar sojin ta ce tana ci gaba da gudanar da sintiri da kuma bincike a yankunan da ake zargin ‘yan ta’addan sun fake, domin tabbatar da cikakken zaman lafiya a arewa maso gabashin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *