Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Noma da Samar da Abinci ta Ƙasa, Dakta Marcus Ogunbiyi, ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa Taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 80 a Sashen Kwamiti na Biyu da ke kula da Harkokin Tattalin Arziki da Kuɗi a birnin New York.
Tawagar ta Najeriya ta halarci zama na fasaha kan noma, samar da abinci da kuma abinci mai gina jiki, inda suka jaddada aniyar Najeriya wajen taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin duniya na magance yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Dakta Ogunbiyi ya bayyana manufofi da shirye-shiryen da ake aiwatarwa a Najeriya domin ƙarfafa noma, samar da kayan aiki ga manoma, da kuma tabbatar da juriyar tsarin abinci kan matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.
Ya ce, Najeriya na aiki ba kawai don tabbatar da wadatar abinci ga ‘yan ƙasa ba, har ma da taka muhimmiyar rawa wajen tsara hanyoyin dorewa don magance ƙalubalen samun abinci a duniya.
Zaman ya tattaro manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na duniya domin musayar ra’ayoyi da dabaru wajen cimma manufofin ci gaba masu dorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya (SDGs), musamman burin kawar da yunwa nan da shekarar 2030.
Halartar Najeriya alama ce ta ƙarin jajircewa wajen daidaita manufofin samar da abinci a ƙasa da kuma tsarin ƙasa-da-ƙasa don ci gaba mai dorewa da shigar kowa.