Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa matuƙa tare da jajanta wa iyalai da dangin ɗalibai mata da aka sace daga Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu, a Jihar Kebbi.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Litinin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce: “Muna cikin damuwa, kuma mun ƙudiri aniyar dawo da ‘yan matan gida lafiya.”
Ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nanata cewa kare kowane ɗan Nijeriya, musamman ɗaliban makaranta, haƙƙi ne da ya rataya a kan gwamnati.
Idris ya ce: “Gwamnati ta yi Allah-wadai da wannan mummunan harin da aka kai kan ɗaliban da kuma kashe ma’aikatan makarantar waɗanda suke gudanar da aikin su mai daraja.”
Ya ƙara da cewa: “An bai wa jami’an tsaro da na leƙen asirin mu umarnin da su nemo, su ceto, kuma su dawo da ɗaliban lafiya, kuma su tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.
“Gwamnatin Tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an cimma wannan buri.
“Muna tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa ƙarfafa tsaron cikin gida muhimmi ne a gare mu. Gwamnatin Tarayya tana sake fasalin sojojin ƙasar nan, ‘yan sanda, da kuma tsare-tsaren jami’an leƙen asiri domin hana irin waɗannan hare-hare, da kuma bada amsa da sauri da kuma daidaito a duk lokacin da barazana ta taso.
“Har ila yau, Nijeriya tana ƙarfafa haɗin gwiwa da abokan hulɗar yanki ta hanyar ECOWAS, Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU), da kuma Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasashe Daban-Daban (MNJTF) don tabbatar da tsaron iyakokin mu da kuma lalata cibiyoyin ‘yan ta’adda da na masu aikata laifuka.
“Muna roƙon jama’a da su kwantar da hankalin su, su kasance cikin juriya.”
