Wasan ƙarshe na AFCON 2023 a yau: NOA ta shiga gangamin tara wa Super Eagles ɗimbin magoya baya – Idris
Yayin da ake ta shirye-shiryen karawa tsakanin ƙungiyar Super Eagles ta Nijeriya da Elephants na Ivory Coast a wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Afrika na bana (AFCON 2024), tuni Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar Da da Kai ta Ƙasa (NOA) ta fara gangamin tara wa ‘yan wasan Nijeriya ɗimbin magoya baya a dukkan jihohin…
