Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta saki Bafalasdinen da ya fi kowanne dadewa a kurkukun ta
Bafalasdinen da ya fi kowanne dadewa a kurkukun Haramtacciyar Kasar Isra’ila, Nael Barghouti, wanda ya yi sama da shekaru 40 a kurkuku, ya shaki iskar ‘yanci a ranar Alhamis karkashin musayar ‘yan kurkuku da wadanda aka yi garkuwa da su…
Makiyaya hudu sun rasu bayan cin kifin da ake zargin na dauke da guba a Taraba
Fulani makiyaya mutum hudu da aka bayyana sunansu da Abdul Juli, Sule Abubakar, Adamu Mato da Saidu Payo sun rasu a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba bayan ruwaito cewa sun dafa tare da cin kifin da suka tsinta…
Natasha ta kai Akpabio kotu tare da neman biyan diyyar naira biliyan 1 da miliyan 300
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da karar shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio kan ikirarin bata suna. Kamar yadda PM News ta ruwaito, karar wadda aka shigar a babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja a ranar 25 ga watan Fabrairun…
Hukumar yaki da safarar mutane a Nijeriya ta ceto mutane sama da 20,000 a shekaru 22
Shugaban hukumar NAPTIP, Binta L. Adamu Bello
Surukar Ministan Yaɗa Labarai ta Rasu
A daren jiya Allah ya ɗauki ran Hajiya Hauwa, surukar Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris. Mahaifiyar maiɗakin Ministan ta rasu ne sakamakon rashin lafiya, tana da shekaru 70 a duniya. Mataimaki na Musamman ga Ministan,…
ISMA ta shirya taron fadakarwa kan lafiya a lokacin azumin Ramadan a Katsina
Sashen Kula da Lafiya na Harkar Musulunci a Najeriya (ISMA) ya shirya taron fadakarwa don ilmantar da al’ummar musulmi kan yadda za su kula da lafiyarsu yayin azumin Ramadan. Taron, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025,…
Sheikh Ibraheem Zakzaky na daga cikin dubban mahalarta jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah a Lebanon
Dubban jama’a, jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, malamai da shugabanni daga kasashe sama da 70 ne suka halarci jana’izar tsohon babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyid Hassan Nasrallah, a kasar Lebanon. Kamar yadda kafar watsa labaru ta Daily…
Dubunnan mutane suka halarci jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah, Safieddine a Lebanon
Gomomin dubunnan masu makoki ne suka taru a filin wasan da ya fi kowanne girma a kasar Lebanon a ranar Lahadi domin halartar jana’izar babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyid Hassan Nasrallah da magajinsa, Hashem Safieddine, wadanda dukkaninsu Haramtacciyar Kasar Isra’ila…
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Gwamna Bago murnar cika shekara 51
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umar Bago, murnar cikar sa shekara 51 a duniya. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Idris ya yaba wa…
Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da zauren tattaunawa na ministoci karo na biyu
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fara zagaye na biyu na Zauren Tattaunawa na Ministoci, inda Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Eshiokpekha Momoh, da Ƙaramin Ministan sa, Alhaji Uba Maigari…










