ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

Nijeriya za ta nuna gyare-gyaren tattalin arzikin Tinubu a taron kasuwanci a Faransa

Gwamnatin Nijeriya za ta yi amfani da damar da ta samu ta halartar Taron Kasuwanci na Faransa da ke tafe a birnin Paris don bayyana irin cigaban tattalin arzikin da aka samu ƙarƙashin shugabancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, a cewar…

Nijeriya ta samu damar karɓar baƙuncin taron hulɗa da jama’a na duniya na 2026

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) murna kan samun damar karɓar baƙuncin Taron Hulɗa da Jama’a na Duniya (World Public Relations Forum, WPRF) na shekarar 2026….

Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na Chana – Ministan Yaɗa Labarai

Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin fahimtar juna guda biyu da aka rattaba wa hannu tsakanin Hukumar Watsa Labarai ta ƙasar Chana (China Media Group) da Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN) a…

Kasashen Faransa, Ingila da Jamus sun yi kira ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kasashen Faransa, Ingila da Jamus a ranar Laraba sun nemi Haramtacciyar Kasar Isra’ila (HKI) da ta tabbatar da “rashin tsaiko” ga shigar da kayayyakin taimakon jin kai zuwa yankin Falasdinawa na Gaza da yaki ya yiwa illa, inda suka yi…

Kasafin kuɗin 2025 taswira ce ta ƙarfafa tattalin arziki da cigaban ƙasa – Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗi na 2025 a matsayin wata muhimmiyar taswira ta ƙarfafa tattalin arziki, daidaito na zamantakewa, da cigaban ƙasa. Da yake jawabi a Taron Manema Labarai na Ministoci…

Mambobin Basij biyu sun rasu biyo bayan kai masu hari a Iran

Mambobi biyu na rundunar tsaro ta Basij da ke karkashin rundunar kare Juyin-juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) da ke Iran sun rasa rayukansu a ranar Asabar sakamakon hari da aka kai masu a yankin da ke fama da tashe-tashen…

Ramadan: Tsare-tsare na sun rage farashin abinci, sun kawo sauki ga Musulmin Nijeriya – Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Juma’a ya yi ikirarin cewa yanzu farashin abinci ya sauka, wanda hakan ya samar da sauki ga Musulmi masu gabatar da azumin watan Ramadan a yayin da ake tsaka da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki…

Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta saki Bafalasdinen da ya fi kowanne dadewa a kurkukun ta

Bafalasdinen da ya fi kowanne dadewa a kurkukun Haramtacciyar Kasar Isra’ila, Nael Barghouti, wanda ya yi sama da shekaru 40 a kurkuku, ya shaki iskar ‘yanci a ranar Alhamis karkashin musayar ‘yan kurkuku da wadanda aka yi garkuwa da su…

Makiyaya hudu sun rasu bayan cin kifin da ake zargin na dauke da guba a Taraba

Fulani makiyaya mutum hudu da aka bayyana sunansu da Abdul Juli, Sule Abubakar, Adamu Mato da Saidu Payo sun rasu a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba bayan ruwaito cewa sun dafa tare da cin kifin da suka tsinta…

Natasha ta kai Akpabio kotu tare da neman biyan diyyar naira biliyan 1 da miliyan 300

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da karar shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio kan ikirarin bata suna. Kamar yadda PM News ta ruwaito, karar wadda aka shigar a babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja a ranar 25 ga watan Fabrairun…