Iyalan Askarawan Zamfara da suka rasu za su sami tallafin da ya dace, in ji Gwamna Dauda Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya da tallafi ga iyalan ’yan Rundunar Kare Jama’a ta Zamfara (CPG) ‘Askarawan Zamfara’ da suka rasa rayukansu a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga.

A ranar Alhamis ɗin nan da ta gabata ne aka gudanar da bikin karrama wasu jami’ai 20 na ‘Askarawan Zamfara’ da lambobin yabo bisa ƙwazon da suka nuna a lokacin gudanar sa ayyukan su. An gudanar da bikin ne a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da aka ƙawata sun taka rawar gani sosai.

A cewar sanarwar, jami’an da aka yi wa adon suna ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed ne, Kwamandan Rundunar Kare Al’umma ta jiha.

“A ranar Alhamis, Gwamna Dauda Lawal ya yi wa jami’ai 20 waɗanda suka taka rawar gani wajen gudanar da ayyukansu ado da lambobin yabo. Dukkanin 20 ɗin sun kasance gwanaye a fagen yaƙi da ‘yan bindiga domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.”

A yayin jawabin nasa, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada sadaukarwar gwamnatinsa wajen jin daɗin Askarawan Zamfara tare da yin alƙawarin bayar da cikakken goyon baya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

“Ku yi la’akari da yi muku ado a matsayin wata hanya ta zaburar da ku don ƙara himma a cikin wannan muhimmiyar sadaukarwa da ku ke yi.

“Ba za mu iya biyan ku kan hidimar da ku ke yi wa ƙasa da bil’adama ba; Abin da kawai za mu iya yi shi ne ƙarfafawa don jin daɗin ku.

“Ina so in tabbatar muku da cewa muna da wani shiri da aka yi wa iyalan ’yan Rundunar Kare Jama’a da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Za mu biya musu dukkan buƙatunsu da kuma ba su dukkan tallafin da ya dace.”

Tun da farko, Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed, kwamandan Rundunar Kare Al’umma, ya bayyana cewa an zaɓo jami’ai 20 ne daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar bisa yadda suka nuna ƙwazo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *