Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a yi gaggawar dakatar da fitar da makamai zuwa Isra’ila

Hoto: Francesca Albanese, mai rahoto ta musamman ta majalisar dinkin duniya a kan halin da hakkin dan Adam ke ciki a yankunan Falasdinawa da aka mamaye

Mai rahoto ta musamman ta majalisar dinkin duniya kan halin da hakkin dan Adam ke ciki a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, na yin kira ga bukatar da ake da ita na dakatar da fitar da makamai zuwa Isra’ila, kamar yadda ta bayyana a ranar Talata.

Kamar yadda the New Arab ta ruwaito, mai rahoton ta ce halin da ake ciki a Gaza bai canza ba tun bayan hukuncin kotun duniya da ya nemi da a gurfanar da Isra’ila.

“Irin mummunan halin da mutanen Gaza ke fuskanta ba za a iya bayyana shi ba, kuma yanayin na kara munana a gabar yamma da kogin Jordan, kuma majalisar dinkin duniya dole ta dauki nauyin ta na aikin agaji tare da samar da tsaro ga fararen hula.” Kamar yadda Albanese ta bayyana.

A wani bangaren, kafar ta ruwaito cewa harin jirgin yakin Isra’ila ya kashe dan jaridar Falasdinawa Mohammed al-Jamal bayan da harin jirgin ya samu gidansa a Rafah a ranar Alhamis, kamar yadda ofishin watsa labaru na Gaza ya bayyana a cikin wani jawabi. Al-Jamal mai kawo rahoto ne na kafar watsa labaru ta Palestine Now News agency.

Rasuwar Al-Jamal ita ta sa kididdigar ‘yan jaridu da suka rasu ya kai 141 tun bayan 7 ga watan Oktoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *