NELFUND: JAMI’AR TARAYYA TA DUTSIN-MA TA KARBI NAIRA BILIYAN 1.06 DOMIN BIYAN KUƊIN DALIBAI 10,018

Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, da ke Jihar Katsina, ta bayyana cewa ta karɓi Naira biliyan 1,065,391,000 daga Hukumar NELFUND domin biyan kuɗin karatu na dalibai 10,018. Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata wasika da mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Aminu Ado, ya aikawa Daraktan Ayyuka na Hukumar NELFUND.

Bisa ga bayanin jami’ar, kuɗin da aka karɓa za su taimaka wajen tabbatar da cewa dukkan daliban da abin ya shafa sun sami damar ci gaba da karatunsu ba tare da tangarda ba. Wannan mataki na cikin tsarin gwamnatin tarayya na tallafawa dalibai da rage musu nauyin kuɗin makaranta.

Jami’ar ta yi godiya ga hukumar NELFUND da Gwamnatin Tarayya bisa wannan tallafi, tare da bayyana cewa hakan zai inganta cigaban ilimi da tallafawa marasa galihu a fadin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *