Shirin Cusa Ɗa’a da Kishin Ƙasa ya fitar da Daftarin Yaɗa Kyawawan Ɗabi’un Farfaɗo da Martabar Nijeriya

Hoto: Daga hagu: Darakta-Janar na NTA, Malam Abdulhamid Dembos; Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, Shugaban Kwamitin Tsara Daftarin Cusa Ɗa’a a Zukatan Jama’ar Ƙasa, Dakta Mohammed Auwal Haruna, Darakta-Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace, lokacin da shugaban kwamitin ke miƙa kundin daftarin ga Ministan a Abuja a ranar Talata

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya karɓi daftarin yaɗa kyawawan ɗabi’u da cusa ɗa’a domin farfaɗo da martabar Nijeriya.

Da ya ke karɓar daftarin da ya ce zai cusa ɗa’a a zukatan jama’a, Idris wanda a cikin Disamba ya kafa kwamitin tsara daftarin mai mutum 10, ya ce Shugaba Bola Tinubu ne zai ƙaddamar da shirin a cikin wannan shekarar.

A jawabin sa yayin karɓar daftarin daga hannun Shugaban Kwamiti, Dakta Auwal Haruna, a ranar Talata a Abuja, ministan  ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙudiri aniyar zayyana kyawawan ɗabi’un da za a cusa ɗa’a a zukatan jama’a ba tare da la’akari da nuna bambanci ko fifita wata ƙabila ko matsayi ba.

Kakakin Yaɗa Labaran Ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, sh ne ya fitar da sanarwar bayanin bayan taron karɓar daftarin a gaban sauran ‘yan kwamitin.

Idris ya ce: “Shi muhimmancin Daftarin Ɗa’a da Kishin Ƙasa gwamnati ce a kan gaba wajen ɗabbaƙa shi.”

Abin Da Daftarin Ya Ƙunsa:

Ministan ya ce daftarin ya ƙunshi Alƙawurra Bakwai da Nijeriya ta ɗaukar wa ‘yan ƙasar ta, sai kuma wasu Ƙudirori Bakwai da ‘yan Nijeriya ya za su ɗauka wajen kare martabar ƙasar su.

Ya ce daftarin zai tafi tare da yin la’akari da irin ɗimbin yawan matasan da wannan ƙasa ke da shi, waɗanda ke rayuwa duniyar da ƙirƙire-ƙirƙiren fasahar zamani ke da tasiri a duniya.

A kan haka ne ya ce gwamnati ta ƙudiri aniyar tabbatar da cewa matasa za su ja ragamar ƙoƙarin bunƙasa ƙasar nan domin samun dauwamammen cigaba.

Ministan ya yaba wa ƙoƙarin da gwamnatocin baya su ka yi wajen haƙilon neman hanyoyin da za a bi domin magance sakwarkwacewar kyawawan ɗabi’u a zukatan ‘yan Nijeriya, ta hanyar bijiro da shirye-shirye daban-daban a baya, irin su “Nigeria: Good People, Great Nation”, “Change Begin With Me”, da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *