ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

Surukar Ministan Yaɗa Labarai ta Rasu

A daren jiya Allah ya ɗauki ran Hajiya Hauwa, surukar Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris. Mahaifiyar maiɗakin Ministan ta rasu ne sakamakon rashin lafiya, tana da shekaru 70 a duniya. Mataimaki na Musamman ga Ministan,…

ISMA ta shirya taron fadakarwa kan lafiya a lokacin azumin Ramadan a Katsina

Sashen Kula da Lafiya na Harkar Musulunci a Najeriya (ISMA) ya shirya taron fadakarwa don ilmantar da al’ummar musulmi kan yadda za su kula da lafiyarsu yayin azumin Ramadan. Taron, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025,…

Sheikh Ibraheem Zakzaky na daga cikin dubban mahalarta jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah a Lebanon

Dubban jama’a, jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, malamai da shugabanni daga kasashe sama da 70 ne suka halarci jana’izar tsohon babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyid Hassan Nasrallah, a kasar Lebanon. Kamar yadda kafar watsa labaru ta Daily…

Dubunnan mutane suka halarci jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah, Safieddine a Lebanon

Gomomin dubunnan masu makoki ne suka taru a filin wasan da ya fi kowanne girma a kasar Lebanon a ranar Lahadi domin halartar jana’izar babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyid Hassan Nasrallah da magajinsa, Hashem Safieddine, wadanda dukkaninsu Haramtacciyar Kasar Isra’ila…

Ministan Yaɗa Labarai ya taya Gwamna Bago murnar cika shekara 51

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umar Bago, murnar cikar sa shekara 51 a duniya. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Idris ya yaba wa…

Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da zauren tattaunawa na ministoci karo na biyu

Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fara zagaye na biyu na Zauren Tattaunawa na Ministoci, inda Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Eshiokpekha Momoh, da Ƙaramin Ministan sa, Alhaji Uba Maigari…

Jihar Taraba ta mayar da shanu 198 da aka sace ga masu su

Jihar Taraba ta mayar da shanu 198 wadanda rundunar 6 Birget na sojin Nijeriya da kuma mafarautan kauye suka kama a jihar da aka sato ga masu su. Sojojin na rundunar 6 Birget a ranar 27 ga watan Janairun 2025…

Shugabannin larabawa sun hadu a Saudi Arabiya domin tunkarar shirin Trump

Shugabannin larabawa sun hadu a Saudi Arabiya domin tattaunawa a kan shirin sake gina Gaza da ke da niyyar tunkarar shirin shugaban kasa Donald Trump na Amurka ta mallake zirin tare da tursasa tashin al’ummar Falasdinawa da ke cikinsa, kamar…

Daluba daya ta rasu, 4 sun jikkata bayan fadowar katanga kan dalubai a jihar Yobe

Halima Ibrahim, daluba da ke aji biyu na babbar sakandaren kimiyya da fasaha ta ‘yan mata da ke Potiskum, ta rasu a ranar Alhamis bayan fadowar da ginin makarantarsu ya yi suna tsakar daukar darasi. Kamar yadda PM News ta…