ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

‘Yan sanda sun kama matasa 20 da makamai masu hatsari a jihar Ogun

‘Yan sanda sun kama matasa 20 da makamai masu hatsari kan iyakar jihohin Ogun da Oyo a ranar Asabar. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, CSP Omotola Odutola, ce ta bayyana haka a ranar Asabar a cikin…

Shugaba Tinubu A Taron AU

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗau hoto tare da sauran Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci a wajen Zama na 38 na Taron Babbar Majalisar Ƙungiyar Haɗa Kan Afrika (AU) a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha a ranar wannan Asabar ɗin….

Kasar Sin ta yi gargadi ga kasashen Amurka da Indiya

Kasar Sin ta gargadi Amurka da Indiya da su gujewa amfani da kasar Sin wajen yin fito-na-fito ta hadaka biyo bayan sanarwar Amurka na kara yawan sayar da makamai ga Indiya. Kamar yadda Press TV ta ruwaito, mai magana da…

Falasdinawa 369 za su fito daga kurkukun Haramtacciyar Kasar Isra’ila a ranar Asabar

Haramtacciyar Kasar Isra’ila za ta sako Falasdinawa 369 da ke tsare a kurkukun ta a ranar Asabar a karkashin musayar fursunoni kashi na shida a Gaza, kamar yadda The New Arab ta ruwaito kungiyar da ke fafutika ta Falasdinawa ‘yan…

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin Tigran Gambaryan kan jami’an gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Ba’amurken nan Mista Tigran Gambaryan ya yi kan wasu jami’an gwamnatin Nijeriya, tana mai bayyana shi a matsayin ƙarya da yaudara. Gambaryan dai jami’in kamfanin Binance ne daga Amurka, wanda hukumar EFCC ta gurfanar…

Jami’an tsaro sun dakatar da taron Nisfu Sha’aban a Abuja

..Amma an canza wuri Jami’an tsaro cikin shirin yaki sun dakatar da taron Nisfu Sha’aban da ‘yan’uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky suka fara gabatarwa a Abuja a ranar Juma’ar nan. Da misalin karfe 3 na ranar Juma’a 15 ga Sha’aban…

Wane bom ne GBU-43 MOAB da Amurka za ta ba Haramtacciyar Kasar Isra’ila?

Shugaban kasar Amurka Donald Trump kamar yadda aka ruwaito ya amince da kai bama-bamai masu nauyin ton 11 da ake kira “Mother of All Bombs (MOAB)” zuwa ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila, wani mataki wanda shugabannin Amurka gabaninsa suka ki yarda…

Ranar Rediyo ta Duniya: Minista na so gidajen rediyo su wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga gidajen rediyo a faɗin Nijeriya da su yi amfani da kafafen su wajen ilimantar da jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa. A cikin wata sanarwa…

Dakatar da agaji da Trump ya yi ya jefa dubunnan mutane cikin yunwa a Sudan

Bayan ya yi sanadiyyar rasuwar dubunnan mutane da tayar da miliyan 12 daga muhallansu, yakin Sudan ya jefa yankuna biyar na kasar cikin yunwa, kamar yadda The New Arab ta ruwaito. Sai dai kamar yadda kafar watsa labarun ta bayyana,…

Allah Ya yiwa shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano rasuwa

Allah Ya yiwa shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Danzago rasuwa. Kamar yadda kafar watsa labaru ta Aminiya ta ruwaito, Marigayi Alhaji Ahmadu Haruna ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya kuma daya daga cikin…