Shugaban Rundunar Tsaron Najeriya (CDS), Laftanar Janar Christopher Musa, ya gargadi duk wani ɗan Najeriya da ke taimaka wa ’yan ta’adda, da cewa gwamnati za ta ɗauki mataki mai tsauri a kansu.
A cewarsa: “Masu taimaka wa ‘yan bindiga da rahotanni ko kayan aiki, ku sani, abokin barawo barawo ne. Don haka ba za mu bar ku ba.” Musa ya bayyana hakan ne a wajen taron Sir Ahmadu Bello Foundation da ya gudana a Arewa House a Kaduna.
Hakazalika, ya kuma ce akwai cikakken haɗin kai tsakanin Najeriya da makwabtan ƙasashe irin su Nijar da Benin wajen tabbatar da tsaro a yankin Sahel da Arewa. Ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa yana ƙara ƙarfafa matsayinsu wajen magance barazanar ta’addanci.
